Bala ya naɗa Gamawa Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Bauchi

Daga WAKILINMU

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya naɗa Dr Aminu Gamawa a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar da ke Bauchi.

Gamawa ya maye gurbin Ladan Salihu ne wanda  aka sauke daga muƙaminsa a ran 9 ga Yuni, tare da Sakataren Gwamnatin Jihar, kwamishinoni da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa.

Mai bai wa gwamna shawara kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Mukhtar Giɗaɗo, shi ne ya bayyana naɗin Gamawa cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Litinin a Bauchi.

Kafin naɗin nasa, Gamawa shi ne Kwamishinan Ma’aikatar Kasafi da Tsarin Tattalin Arziki.


Sanarwar ta ce Gamawa ya yi aiki a wurare da dama kuma a fannoni daban-daban.