NUJ ta samu tabarrukin Janar Babangida a Minna

Daga BASHIR ISAH

Tsohon Shugaban Ƙasa, Ibrahim Badamasi Babangida, ya bai wa Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ) Reshen Jihar Neja, tabbacin mara mata baya don taimaka mata wajen cim ma manufofinta.

Babangida ya ba da wannan tabbaci ne a lokacin da tawagar sabbin shugabannin NUJ na jihar Neja ta ziyarce shi a gidansa da ke Minna, a Lahadin da ta gabata.

Tsohon shugaban ya ce ya yaba da ziyarar ‘yan jaridar ƙarƙarshin jagorancin shugabansu na jiha, Comrade Abu Nmodu. Tare da kira a gare su da su kasance masu aiki da gaskiya a kowane lokaci.

Haka nan, ya shawarce su da su yi aiki tukuru don cimma kyawawan manufofin da suka sanya a gaba. Yana mai cewa, a shirye yake ya mara musu baya wajen ganin haƙarsu ta cim ma ruwa a kowane hali.

Tun farko sa’ilin da yake jawabi, shugaban ƙungiyar Comrade Abu Nmodu, ya shaida wa tsohon shugaban ƙasar cewa sun kai ziyarar ne domin neman albarkar magabata.

Ya bayyana cewa sabon shugabancin ƙungiyar na da niyyar kawo sauye-sauye na cigaba a harkar jarida a jihar Neja kuma daidai da zamani.

Daga nan, Abu Nmodu ya yi amfani da wannan dama wajen neman Babangida ya tallafa ya gyara musu Cibiyar ‘Yan Jarida da ke Minna wadda aka yi wa inkiya da sunansa, domin ba su damar gudanar da harkokinsu a cibiyar yadda ya kamata.