Ban taɓa sa ran zan zama shugaban APC na ƙasa ba, cewar Sanata Adamu

Daga BASHIR ISAH

Bayan kwanaki huɗu da zaɓensa a matsayin shugaban APC ƙasa Sanata Abdullahi Adamu ya karɓi ragamar aiki inda zai ci gaba da jagorancin harkokin jam’iyyar tasu ta APC a matsayin sabon shugabanta.

Adamu, wanda ya isa sakatariyar Jam’iyya da misalin ƙarfe 10:30am na ranar da ya ƙarɓi ragamar aiki, ya ce kimanin wata guda da ya gabata bai taɓa kawowa a ransa cewa zai zama shugaban jam’iyya ba.

Turakin Keffi ya zama ɗan takarar jam’iyya ne ba tare da hamayya ba kasancewar shi ne zaɓin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari wanda daga bisani dukkan masu kwaɗayin kujerar suka yi masa mubaya’a.

Da yake jawabi a wajen bikin karɓar ragamar aiki a Abuja a ranar Larabar da ta gabata, tsohon Gwamnan Jihar Nasarawar ya ce, ganin cewa ƙasa da watanni 12 ya rage kafin babban zaɓe na ƙasa ya zama wajibi a haɗa kai a yi aiki tare don tabbatar da nasarar jam’iyya saboda a cewarsa Shugaba Buhari ba zai lamunci shan kaye ba.

Ya ce, “Yin Allah ne da muka zama sabbin shugabannin gudanarwar jam’iyyarmu (NWC). Ga shi dai abu ne mai sauƙi a zahiri, amma dai yin Allah ne ba yinmu ba.

“Wata guda da ya gabata, ban san cewa ni ne zan zama sabon ciyaman na APC ba. Yau ga ni ina karɓar ragamar aiki daga shugaban jam’iyya mai barin gado. Allah kaɗai ke da ikon aiwatar da wannan. Ba hikimata ba ce ko kuma ƙarfina.

“A madadin sabbin ‘yan kwamitin NWC, ina mai cewa lamarin ba abu ba ne mai sauƙi a gare mu. Muna da babban al’amari a gabanmu wanda da shi ne za a gwada gudun ruwanmu, wato babban zaɓe mai zuwa. Ni dai a gare ni, yayin da muka soma aiki, babban aikin da za mu fuskanta shi ne yadda za nu yi ɗawainiyar zaɓuɓɓukan a matsayinmu na jam’iyya.”

Tun farko sa’ilin da yake jawabi a wajen bikin, tsohon shugaban riƙo na APC, Gwamna Mai Mala Bini, ya bayyana irin nasarorin da suka samu a lokacin da jam’iyyar ke ƙarƙashin kulawar su.