Matsalar watsi da manyan ayyukan raya ƙasa

A cikin wasu ’yan shekaru da suka gabata, Shugaban Ma’aikatar tantancewa tare da kula da kwangilolin gwamnati (Bureau of Public Procurement), Injiniya Emeka Eze, ya bayyana wa Majalisar Dattijai cewa, akwai kimanin ayyuka 19,000 a wurare daban-daban na faɗin ƙasar nan da aka yi watsi da su.

Waɗannan ayyuka, sun haɗa da na Gwamnatin Tarayya da kuma na jihohi waɗanda ko dai gwamnati da ta fare su ba ta samu damar kammalawa ba, ko kuma gwamnatin da ta gaji ayyukan ta yi watsi da su. Ko shakka babu, akwai yiwuwar adadin nasu ma ya fi haka da ba don Shugaban ƙasa na yanzu Muhammadu Buhariuhari ya fito da wani tsari na yunƙurin kammala ayyukan da gwamnati ta gada ba, inda ya yanke shawarar ƙarasa ayyukan da ya gada daga tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan.

Har ila yau, ire-iren waɗannan ayyuka da aka yi watsi da su mafi yawancin su a manyan birane ne da ƙananu na Gwamnatin Tarayya da jihohi, sannan abu ne da ya samo asali tun bayan samun ’yancin kan wannan ƙasa a 1960. Kazalika, ayyukan sun haɗa da Manya-manya tituna, dam-dam na ruwa, tashar filin jirgin sama da na ruwa, ginin Makarantu, gine-ginen Ofisoshi da sauran makamantan su.

Abubuwan da ka janyo irin waɗannan matsaloli na yin watsi da manyan ayyukan gwamnati sun haɗa da rashin yin kyakkyawan tsari na ayyukan da kuma ware kuɗin da za a yi amfani da shi, rashin zuba kuɗi a aikin yadda ya kamata, rashin yin aiki mai inganci, cin amana da rashin gaskiya na ’yan kwangila da dai sauran su. Kazalika, akwai kuma matsalar yin watsi da ayyukan musamman ma ga mutanen da ke yin adawa da wannan gwamnati, ba da kwangiloli daga gwamnatin da wa’adinta ya kare tare haramar kwashe kayanta ta yi gaba da sauran makamantansu.     

Ire-iren waɗannan matsaloli sun zama ruwan-dare musamman a wurin gwamnonin da wa’adin mulkinsu ya kare. Dalili kuwa, mafiya yawan ayyukan da su kan bijiro da su, ba su da lokaci da kuma kudin da za su iya aiwatar da su a ɗan lokacin da ya rage musu. Don haka, dole c eke sa waɗanda suka gaje su su tsayar da ayyukan, su kuma sa ’yan kwangila su maido da ’yan kuɗaɗen da a ka ba su don fara aiwatar da aikin.

A matsayinmu na Kamfani wannan gidan Jarida, daga yanzu za mu ɗauki wasu matakai a kan gwamnonin da wa’adin mulkinsu ya kare kamar yadda muke ƙalubalantar waɗanda suka gaje su a kan zargin qin kammala ayyukan nasu da suka gada, don kyautata cigaban ƙasa da kuma ƙoƙarin rage yawan asarar da ake yi na dukiyar al’ummar wannan ƙasa. 
   
Haka nan, saba yin watsi da ayyukan gwamnati kamar yadda aka saba yi a baya a namu ra’ayin, babu abin da ya ke haifarwa illa tsana tare da rashin jituwa tsakanin gwamnatoci da al’ummar da suke mulka. Kazalika, ya haifar da asarar dukiyar al’umma da ɓata lokaci da kuma asarar kuɗaɗen da aka fara bai wa ’yan kwangila don soma aikin.

A nan, mu na sake jan hankalin gwamnoni wajen ƙoƙarin riƙa sake tantance irin waɗannan ayyuka, musamman sakamakon samun hauhawar farashin kayan aiki da sauran su, sannan wajibi ne su riƙa yin irin nasu ’yan dabarun don kammala waɗannan ayyuka da suka gada.

Har wa yau, akwai wata hanyar da ya kamata a riƙa bi don magance wannan dai matsala a namu ganin, ta hanyar yin doka da kuma aiwatar da ita, cewa duk gwamnatin da ta gaji wasu ayyuka daga gwamnatin da wa’adinta ya qare, wajibi ne ta qara waɗannan ayyuka da ta gada. Aiwatar da wannan doka ko shakka babu zai tilastawa gwamnatocin da ke watsi da ayyukan da suke gada wajen kammala su da kuma ba su irin muhimmancin da ya kamata.

Haka zalika, ya na da kyau gwamnatoci su riƙa sauraren shawarwarun ƙwararrun masana da kuma masu ruwa da tsaki, musamman idan suka bayar da shawara a kan abin da suke da ƙwarewa ko masaniya a kai. Yin hakan ba ƙaramin taimakawa zai yi idan ana sauraronsu ana kuma yin aiki da shawarwarinsu ba.    
Wani bincike da aka aiwatar kwana-kwanan nan, ya tabbatar da cewa a Jihar Legas kaɗai, Gwamnatin Tarayya na yin asarar Naira biliyan 126.2 a kan gine-ginen da aka fara yi ba a kammala ba, don kauce irin wannan asarar maƙudan kuɗaɗe, muna baiwa Gwamnatin Tarayya shawara ko dai a sayar da waɗannan kadarori ko kuma a san yadda za a yi da su.

Babu shakka, wannan ba ƙaramin abin haushi da takaici ba ne, na barin irin waɗannan gine-gine ko watsi da su a kullum ta Allah suna ƙara lalacewa sakamakon rashin yin amfani da kula da su.

Akwai wani masani da ya yi wani nazari kan kuɗaɗen da ake yin asara kaɗai daga babban filin wasa (Stadium) na Legas daga shekara ta 2004 zuwa yanzu, ya kai kimanin Naira biliyan 52.6, ban da kuma wasu kadarori daban-daban da gwamnatin za ta iya riƙa samun kusan Naira biliyan 72, idan aka mayar da su a matsayin gidajen zama na haya.

Barin irin wannan asara ta cigaba, ba ƙaramin koma baya ba ne a wurinnmu. Don haka, ya kyautu gwamnatocinmu na tarayya da jihohi su gaggauta yin wani abu a kai.