Tsadar abinci da fetur duk duniya ne, ba Nijeriya kawai ba – Lai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ce tashin farashin  kayan abinci, man fetur, dizel da sauran kayayyaki ya zama ruwan dare gama duniya, ba wai kawai wata ƙasa guda ɗaya ba.

Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai ranar Litinin a Abuja, ya ƙara da cewa taƙaita matsalar ga Nijeriya kaɗai to ya zama yarfe da tsabagen yaɗa kalaman ƙarya.

Ya ce ƙididdiga da ‘yan adawa da wani vangare na kafafen yaɗa labarai da su ke kwatanta farashin wasu kayan abinci, man fetur, dizel, kafin shekarar 2015 da kuma a halin yanzu, yarfe ne kawai.

“Wannan lissafin dokin rano da ƙididdiga ba gaskiya ba ne. Waɗanda su ke amfani da waɗannan ƙididdiga ba tare da sanya su cikin muhallin ba to ba su san ma mai su ke yi ba.

“Mu ɗauki farashin kayan abinci da man fetur. A duba shafin Google a ga farashin kayan abinci a wasu ƙasashe, musamman Burtaniya da Amurka, za ku ga cewa ya yi tashin gwauron zabi. Ba ma a managar farashin iskar gas ko man fetur,” inji shi.

Ministan ya ƙara da cewa matsalar ƙarancin man fetur da ake fama da ita a faɗin ƙasar nan a ‘yan kwanakin nan ya fara samun sauƙi, yayin da matakan da gwamnati ta ɗauka sun fara aiki.

Ministan ya ce matsalar ƙarancin man fetur da ake fama da ita a faɗin ƙasar nan a ‘yan kwanakin nan ya fara samun sauƙi, yayin da matakan da gwamnati ta ɗauka sun fara aiki.