Bayan karɓo Walida daga DSS akwai buƙatar duba lafiyar ƙwaƙwalwarta – Barista Kabiru

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Barista Kabiru Adamu, lauyan da ya jagoranci fafutukar karɓo matashiya Walida wadda ake zargin wani jami’in DSS ya riƙe na tsawon wani lokaci, ya bayyana cewa yarinyar na fama da matsalar jinya a ƙwaƙwalwarta wadda ke buƙatar kulawa ta musamman daga Gwamnatin Jihar Jigawa.

A cewarsa, bayan an sako Walida tare da miƙa ta ga Gwamnatin Jigawa, an lura da sauyin tunani da halayya a tare da ita, inda a yanzu take ganin masu taimaka mata a baya a matsayin maƙiyanta, yayin da take kallon waɗanda ba su taka rawa wajen taimaka mata ba a matsayin masu alheri gare ta.

Barista Kabiru ya bayyana hakan ne bayan da suka miƙa Walida a hannun Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi ɗan Modi, bayan karɓo ta daga ofishin DSS da ke Abuja. Gwamnan ya jagoranci wata tawaga ta jami’an gwamnatin jihar domin karɓo yarinyar, kamar yadda gidan Rediyon Premier na Kano ya rawaito.

Daga cikin tawagar gwamnatin Jigawa da ta raka gwamnan akwai Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Kwamishinan Shari’a da kuma Kwamishiniyar Harkokin Mata.

Lauyan ya ce wannan mataki na gwamnatin Jigawa ya nuna cewa gwagwarmayar da suka yi ta dogara ne kan gaskiya da neman adalci, duk da ƙoƙarin da wasu suka yi na kare jami’in da ake zargi a lamarin.

Shi ma mahaifin Walida, Malam Abdulhadi Ibrahim, ya bayyana farin cikinsa da yadda aka sako ‘yarsa tare da miƙa ta ga gwamnatin jihar. Ya ce a baya sun je ofishin DSS amma ba a ba su damar ganawa da ita ko yin magana da ita ba.

Malam Abdulhadi ya buƙaci a ba da damar bin diddigin lamarin ta fuskar shari’a, tare da neman taimakon gwamnatin Jigawa da kotu domin tabbatar da an binciki duk wanda ke da hannu a abin da ya kira zalunci da aka yi musu.

Lamarin ya ja hankalin ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da ‘yan jarida, inda suka yi ta muhawara da yayata batun domin a samu cikakken bayani da gaskiya kan abin da ya faru.

A wani ɓangare kuma, masu lura da al’amura sun tuno da wani lamari makamancin haka da ya faru a baya, inda aka tsare wani matashi ɗan asalin Kano mai suna Yunusa Yellow bisa zargin satar yarinya da canza mata addini. Daga baya dai an bayyana cewa ba tilastawa aka yi ba kamar yadda aka fara zargi.

Masu ruwa da tsaki na ci gaba da kira da a tabbatar da an gudanar da bincike cikin gaskiya da adalci, tare da ba Walida kulawar lafiya da ta dace domin tabbatar da dawowar lafiyarta da walwalarta.

By ukarofi