Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Argungu da Augie a zauren majalisar wakilai Honarabul Sani Yakubu yargiwa ya yi kira ga al’umma da su dukufa wajen yi wa kasar nan addu’a ta musamman a wannan lokacin na watan Azumin Ramadan.
Ya yi wannan kiran ne a garin Argungu lokacin da ya ke raba abinci a mazabarsa.
Yargiwa ya ce ba shakka kasar nan tana cikin wani yanayi na damuwa musamman abinda ya shafi tsaro da talauci da ke Addabar al’umma.
Ya bayyana cewa akwai kalubale ga shugabanni musamman wadanda al’umma suka taru suka zabe su bisa ga kyakykyawan zato da su ke yi musu.
Yana da kyau ya kasance kofofin yan siyasa su kasance a bude a ko da yaushe domin karbar shawarwari da kuma korafi domin gabatarwa a zauren majalisa.
Hakazalika su ma al’umma suna da hakkin sanarda hukumomi kan duk wani abu da suka gani kuma ba su yarda da shi ba.
