Bayan shekara 38 da kammalawa, Minista Dare ya ziyarci tsohuwar makarantarsu a Jos

Ministan Harkokin Matasa da Wasannin Motsa Jiki, Sunday Dare, ya ziyarci sakandaren da ya yi karatu a Jos shekaru 38 da suka gabata.

Dare ya ziyarci Baptist High School ne don halartar bikin cika shekara 60 da kafuwar makarantar.

A saƙonsa da ya wallafa a shafinsa na twita, ministan ya ce ziyarar da ya kai makarantar ta tuna masa baya, sannan ɗalian sun cika da murnar ganin sa a tsakaninsu.

An ga ministan a tsakanin ɗalibai sa’ilin da yake yi musu jawabi da kuma lokacin da yake ɓarje rawarsu ta gargajiya tare da wasu daga cikin ɗaliban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *