Mutum 11 sun halaka a harin makaranta a Rasha

Daga UMAR M. GOMBE

Rahotanni daga Ƙasar Rasha sun nuna a ƙalla mutum 11 waɗanda galibinsu yara ne, suka mutu a harin da aka kai wata makaranta da ke yammancin Kazan a ƙasar.

Kamfanin dillancin labarai na RIA da ke ƙasar, ya ruwaito cewa a ƙalla yara 16 zuwa 12 da kuma wasu mayan su 4 ne aka kwantar a asibiti bayan harin a Talatar da ta gabata.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Interfax, wasu ‘yan bindiga biyu ne suka buɗe wa makarantar wuta inda suka yi ta harbin kan mai uwa dawabi.

Hoton bidiyon harin da aka yaɗa a soshiyal midiya, ya nuna ‘yan sanda riƙe da wani matashi a wajen makarantar.

Kazalika, hoton ya nuna yadda jami’an bada agajin gaggawa ke ta kai-komo a yankin domin bada agaji.

Hukumomi sun ce an ɗauki ƙarin matakan tsaro a ɗaukacin makaratun Kazan don hana aukuwar irin haka.

Kai wa makarantu hari a Rasha ba sabon al’amari ba ne. Domin kuwa, ko a 2018 makamancin wannan ya auku inda wani mahari ya hallaka ɗalibai 19 sannan ya juya bindigar ya kashe kansa.