Kalu ya yi tir da harin da aka kai wa ofishin INEC a Abiya

Daga WAKILINMU

Tsohon gwamnan Jihar Abiya wanda kuma shi ne mai tsawatarwa a Majalisar Dattawa, Dakta Orji Uzor Kalu, ya yi Allah-wadai da harin da wasu ɓatagari su ka kai wa ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa na Ƙaramar Hukumar Ohafia da ke jihar.

Shi dai ofishin na INEC, wasu waɗanda ba a san ko su waye ba ne su ka banka masa wuta a ranar Lahadi, inda su ka lalata kayayyakin zaɓe da wasu kadarorin.

A yayin da ya ke bayyana harin da cewa ya saɓa wa tsarin dimokiraɗiyya kuma rashin wayewa ne, Kalu ya yi kira ga jami’an tsaro da su fara cikakken bincike kan harin don su gano waɗanda su ka aikata wannan ta’asar kuma su gurfanar da su a kotu.

Ya nanata cewa tilas ne a kare tsarin mulkin dimokiraɗiyya na Nijeriya da ke tasawa domin a samu cigaba.

A lokacin da ya ke kira ga ‘yan siyasa da su rungumi kyawawan halayen dimokiraɗiyya a al’amuran su, tsohon gwamnan ya kuma nanata cewa ita siyasa ba a yin ta da nufin a mutu ko a yi rai.

Ya ce, “Harin da aka kai wa ofishin INEC na Ƙaramar Hukumar Ohafia ta Jihar Abiya bai da wani hurumi kuma ba za a amince da shi ba.

Ya ce, “Hukumar zaɓe ta Nijeriya, INEC, ta na ƙoƙari wajen gudanar da muhimmin aikin ta na haɓaka tare da gina muradan dimokiraɗiyya a ƙasar nan.

”Masu ɗaukar nauyi da masu aiwatar da wannan hari abokan gabar ƙasar nan ne.

“Ina kira ga hukumomin tsaro da su gano mutanen da su ka aikata wannan hari da nufin hana aukuwar irin sa a nan gaba.”

Kalu ya yi kira ga INEC da kada ta karaya wajen ƙoƙarin da ta ke yi na haɓaka muradan dimokiraɗiyya a Nijeriya.