Daga USMAN KAROFI
Dakarun sojin Najeriya sun tabbatar da dawo da tsaro a hanyar Sheme zuwa Ƙanƙara da ke Jihar Katsina, wadda aka fi sani da hanya mafi haɗari a jihar, sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan bindiga. Hanyar tana da tsawon kilomita 34 kuma na daga cikin hanyoyin fita daga Jihar Katsina zuwa jihar Zamfara.
Wani rangadin ‘yan jarida da aka kai a cikin makon nan ya tabbatar da cewa an jibge jami’an tsaro daga ɓangaren sojoji da ‘yan sanda da sauran hukumomi a muhimman wurare a hanyar, bayan kusan watanni 30 da rashin tsaro ke hana mutane amfani da hanyar.
Hanyar Sheme-Ƙanƙara wadda ke da mahimmanci wajen hada al’ummomin karkara kamar su Ruwan Godiya da Sheme, ta daɗe babu zirga-zirga saboda fargabar tsaro. Sai dai ko da yake an samu sauyi, har yanzu ba a cika amfani da hanyar ba, lamarin da ke haifar da damuwa ga mazauna yankin da kuma shugabanni na cikin gida.
Kwamandan Brigade ta 17 a Jihar Katsina, Birgediya Janar Omopariola, ya ce sojojin sun ƙara ƙaimi a aikin tsaro, kuma hakan ya haifar da sauye-sauye masu ma’ana. Ya buƙaci direbobi da ‘yan kasuwa da su fara amfani da hanyar domin farfado da harkokin kasuwanci. Mazauna yankin sun roƙi gwamnati ta ci gaba da tsaurara tsaro tare da gyara ɓangarorin hanyar da suka lalace domin mayar da ita hanyar amfani kamar da.
