Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban jam’iyyar APC ta ƙasa Dr Abdullahi Umar Ganduje ya gargaɗi shugabannin ƙananan hukumomi na Jihar Katsina da su guji wawure kuɗin al’umma domin amfanin kan su.
Ganduje ya yi wannan gargaɗi ne a Katsina inda ya halarci bikin rantsuwan zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan 34 da ke Jihar Katsina.
Ya ce cin gashin kan da aka ba ƙananan hukumomi ba wai dama ne aka basu na wawure kuɗin al’umma ba.
Shugaban jam’iyyar na APC ya gargaɗe su da su guji ƙauracewa ofishin su,ya ƙara da cewa ba wai sai kason kuɗaɗen su ya iso a ƙarshen wata ba za a gansu a ofis.
Ya ce gwamna Dikko Raɗɗa zai basu kason kuɗaɗen su ɗari bisa ɗari,sai dai zai sa ido yaga yadda suke kashewa da kuma bincika yadda suka kashe kuɗaɗen.
Daga nan Dr Abdullahi Ganduje ya taya shugabannin ƙananan hukumomin murnan cin gashin kansu ta wajen sarrafa kuɗaɗen su.
Bikin rantsuwan da ya gudana a filin wasa na Muhammadu Dikko ya sami halartar manyan jami’an gwamnatin tarayya da na jiha da kuma ɗimbin magoya bayan jam’iyyar APC.
