Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa, ya rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Katsina 34 tare da gargaɗin su akan su guji ɓarnatar da dukiyar al’umma, su kuma gudanar da mulki cikin gaskiya da adalci.
An gudanar da bikin rantsuwar ne a filin wasa na Muhammad Dikko inda gwamnan ya nanata ƙudurinsa na bai wa ƙananan hukumonin goyon baya don gudanar da ayyukansu.
Kazalika shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yaba wa Raɗɗa a cewarsa gwamnan ya gudanar da sahihin zaɓen ƙananan hukumonin jihar 34.
Dr. Ganduje, ya kuma nuna jin daɗin sa da yadda aka gudanar da zaɓen, yana mai cewa bai yi mamakin nasarar jam’iyyar ba, la’akari da ayyukan ci gaba da gwamna Raɗɗa ke aiwatarwa, musamman a fannin samar da ilimi, tsaro, da kuma siyasa.
Sabbin shugabannin ƙananan hukumonin sun karɓi rantsuwar kama aiki ta hannun babban jojin Jihar Katsina, Alhaji Musa Ɗanladi.

Gwamna Raɗɗa ya jaddada cewa Katsina jiha ce ta jam’iyyar APC, kuma jam’iyyar za ta ci gaba da samun nasara bisa irin ayyukan da ake gudanarwa.
Ya buƙaci sabbin shugabannin da su gudanar da shugabanci ba tare da nuna wariya ko bambanci ba, gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta ba su kuɗaɗen gudanar da ayyuka.
Sai dai gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta riƙa bibiyar ƙananan hukumonin don ganin an yi aiki da kuɗaɗen cikin gaskiya ba tare da yin baba kere da dukiyar al’umma ba.
Alhaji Kabir Abdulsalam Shema shugaban ƙaramar hukumar Dutsinma, ya yi magana a madadin sauran sabbin shugabannin da aka zaɓa.
Shema ya yi alƙawarin gudanar mulki bisa gaskiya da adalci tare da yin kira ga jama’a da su ba da goyon baya tare da yin addu’o’i don samun nasarar aiwatar da ayyuka masu ma’ana waɗanda suka shafi talaka kai tsaye.

