Jiga-jigan NNPP a Kano na shirin koma wa APC

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje CON, ya yi ganawa ta musamman da wasu jiga-jigan jam’iyyar NNPP daga Kano.

Waɗanda aka yi ganawar da su sun haɗa da Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Sanata Kawu Sumaila da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano/Kibiya/Bunkure, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Dala Hon. Ali Madaki da tsohon ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Ɗanbatta/Makoda Hon. Badamasi Ayuba.

Wannan na daga cikin shirye-shiryen su na ficewa daga jam’iyyar NNPP dan komawa jam’iyyar APC.

Sanin kowa ne a kwanakin baya an jiyo waɗannan jiga-jigan suna bayyana irin rashin adalcin da jagoran NNPP Kwankwasiyya Dr Rabi’u Kwankwaso ya ke musu.

By ukarofi