Hare-haren Filato: Gwamna Mutfwang ya zargi ƴan bindigar Fulani da kisan kiyashi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya zargi ƴan bindiga daga cikin ƙabilar Fulani da kai hari a ƙauyukan Zikke da Kimakpa a Ƙaramar Hukumar Bassa, inda aka rasa rayukan kimanin mutane 51 a daren ranar Lahadi.

Ya bayyana hakan ne a yayin hira ta gidan telebijin, inda ya ce lokaci ya yi na kawo ƙarshe hare-haren acikin al’umma.

Ya ce, a ranar 13 ga Afrilu aka sake samun wani mummunan harin a Gundumar Kwall da ke ƙaramar hukumar, lamarin da ya haddasa rasa rayuka da ƙone dukiyoyi.

Daga cikin waɗanda suka rasa rayukan nasu akwai mata da yara ƙanana da tsofaffi gami da raunata wasu da dama ba tare da tausayi ba.

Lamarin ya auku ne ƙasa da makonni biyu da faruwar makamancin sa a wasu yankuna na Ƙaramar Hukumar Ɓokkos dake jihar, inda aka kashe sama da mutane 50 da ƙone ɗaruruwan gidaje.

Gwamnan ya yi alwashin cewa, ba za su bari a mayar ƙauyukansu wajen zubar da jinanan al’ummarsu ba, ya na mai cewa an shirya kai hare-haren ne da nufin ɗaiɗaita al’umma da haddasa tashin-tashina a jihar.

By Babaji