Atiku ya zargi Tinubu da gazawa kan hare-haren Borno da Filato

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya zargi gwamantin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gazawa bisa munanan hare-haren da aka kai a wasu yankunan Jihar Filato.

A wani saƙon jimami da aka wallafa a shafin Facebook, Atiku ya bayyana alhininsa ga kisan mutane 47 a ƙauyukan Zikke da Kimakpa dake Gundumar Kwall a Ƙaramar Hukumar Bassa a jihar.

Harin ya biyo bayan makamancinsa ne da aka kai a Ƙaramar Hukumar Ɓokkos, lamarin da ya hura wutar taɓarɓarewar tsaro da jihar da ma ƙasar baki ɗaya.

Ya bayyana kaɗuwarsa ganin yadda ire-iren hare-haren ke yawaita a jihar, ya na mai cewa lallai akwai gazawa daga gwamanti.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce, wajibin farko akan kowacce gwamanti shine samar da tsaro ga rayuka da dukiyoyin al’ummarta, ya na mai bayyana gazawar gwamnatin Shugaba Tinubu.

Haka kuma, Atiku ya koka ga ƙarin hare-haren da ke faruwa Jihar Borno, inda mayaƙan Boko Haram ke cin karensu ba babbaka, ya na mai bada misali da kalaman Gwamnan jihar, Babagana Zulum da Shehun Borno, waɗanda ke nuna yadda ake cigaba da rasa rayuka da wasu yankunan a hannun mayaƙan ƙungiyar.

Har’ilayau, ya shawarci majalisar dokoki da ta samar da dokar da za ta bai wa jihohi damar sama wa jami’an tsaro makaman zamani da za su ƙarfafa tsaro a yankunansu.

By Babaji