Bello Turji ya ce a shirye yake ya miƙa wuya – Janar Christopher Musa

Spread the love

Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa babban ɗan ta’adda Bello Turji ya bayyana shirin miƙa wuya. Wannan ya zo ne bayan da sojoji suka kashe mataimakansa da wasu manyan abokansa, wanda hakan ya sa ya rasa yawancin mutanensa. Janar Musa ya bayyana hakan a shirin “Politics Today” na gidan talabijin na Channels, inda ya ce Turji yana cikin matsanancin hali kuma ya nuna shirin miƙa wuya in sojoji suka tsaya da luguden wuta.

A cewar Janar Musa, “Mun kashe mataimakansa, mun kashe yawancin abokansa, kuma yanzu ya tilasta wa yawancin mutanensa su tafi. Kwanan nan ya fara nuna cewa ba ya son wani abu kuma domin a shirye yake ya miƙa wuya.” Duk da haka, Janar Musa ya nuna cewa duk wanda ya kashe mutane marasa laifi ba za a ɗaga mishi ƙafa ba, inda ya ce, “Mutane irinsa ba za su tsira ba.”

Sojoji sun ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin Bello Turji, inda suka kashe mataimakansa Aminu Kanawa da wasu manyan abokansa kamar Dosso (kanen Turji) da Ɗanbokolo. Har ila yau, an kashe wasu shugabannin ‘yan ta’adda irin su Abu Ɗan Shehu, Jabbi Dogo, Ɗan Kane, Basiru Yellow, da Kabiru Gebe, da sauransu.

Bayanai daga hedikwatar tsaron Ƙasar ta nuna cewa sojoji sun kashe sama da ‘yan ta’adda 24 da suka gudu daga sansanonin Bello Turji a yankunan Gebe da Isa na jihar Sokoto, da kuma Gidan Rijiya a yankin Shinkafi na jihar Zamfara. Wannan ya nuna ci gaban da sojoji ke samu wajen murƙushe ‘yan ta’adda a yankin Arewacin Najeriya.

By ukarofi