Bello Turji ya yi iƙirarin hannu a hare-haren kwanan nan, ya ce sun shirya wa sulhu ko yaƙi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanannen jagoran ‘yan bindiga, Bello Turji, ya yi iƙirarin hannu a sababbin hare-haren da suka auku a kwanan nan akan jami’an tsaro a jihohin Sakkwato da Zamfara, yayin da ya kuma bayyana shirinsa na yin sulhu da gwamnati.

An fitar da wannan batu ne daga wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta a ranar 20 ga watan Yunin 2026, inda aka ga jagoran ‘yan bindigar cikin shiga ta kayan sojoji da rufe fuskarsa tare da ‘yan barandarsa a kewaye da shi.

A jawabinsa, ya yi tsokaci akan ayyukan tsaro a yankin Arewa ta Yamma kuma ya yi bayani akan farmakin juna tsakanin ƙungiyoyin ‘yan bindiga da jami’an tsaro a ƙauyukan da ke shiyyar da ke faruwa.

Ya yi zargin cewa wasu ƙauyuka na fuskantar hare-hare da kuma ƙwace musu shanu da wurare da dama a ƙananan hukumomin Shinkafi da Sabon Birni a Zamfara da Sakkwato.

A cewarsa, ana gallaza wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba akan abin da ya shafi wasu rikice-rikice a ƙauyukan, inda ake kashe su da karɓe musu dabbobi babisa doka ba.

Ya bayyana cewa, ‘yan dabarsa sun ƙaddamar da hare-hare ne akan jami’an tsaro da nufin ramuwa ko mayar da martani akan cutar da ‘yan uwansu da ke zaune a yankunan da ya ambata a iƙirarin nasa.

Kazalika, jagoran ‘yan bindigar ya ce ƙofar sulhu a buɗe take da gwamnati matuƙar ta buƙaci a yi haka, yana mai cewa ‘yan dabarsa a shirya suke su karɓi tayin daga ɓangaren hukumomin gwamnati a madadin cigaba da musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaro.

By Babaji

Leave a Reply