
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada matsayar gwamnatinsa na ƙin yin sulhu da ‘yan bindiga da ke ayyukansu a jihar, inda ya tirje akan cewa hakan ba zaɓi ba ne a jihar.
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana haka ne a wata hira da BBC Hausa da aka ɗauko a Kaduna inda ya jaddada cewa gwamnatin nasa ta ɗauki matakin amfani da ƙarfin soji wajen magance matsalolin ayyukan rashin tsaro a jihar.
A cewarsa, ba su amince wa kowane mutum ko ƙungiya yin sulhu da ‘yan bindiga ba, yana mai cewa dukkan masu yin haka suan yi ne ba da yawun gwamnatin ba.
Ya bayyana cewa, tsarin yin sulhu da ‘yan ta’adda da suka addabi al’umma da kisan gilla da garkuwa da mutane, ba zai taɓa tasiri ba a ƙarƙashin mulkinsa a jihar.
Ya jaddada cewa wajibi ne a tunkari wadannan ɓata-gari da ƙarfin soja domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Zamfara da ma ƙasa baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa, ba yi nasara na a yunƙuri da dama na yin sulhu da ‘yan bindigar, wanda a cewarsa ke ƙara musu ƙwarin-gwiwa a madadin kawo ƙarshen rashin tsaro.
A ƙarshe, ya kirayi mazauna da su cigaba da haƙuri da ba hukumomin tsaro tallafin da ya dace wajen yaƙi da ta’addanci a yankunansu, yana mai nanata aniyarsa ta ganin an murƙushe ta’addanci ba tare da an lallaɓa masu hannu a aciki ba.
