Daga AISHA ASAS
3. Yadda bilicin ke aiki a fata:
Fatar mutum na da sinadarin melanin, wanda ke ba ta launi kuma yana taimaka wa wajen kare fata daga illar rana, cututtuka da kumburi. Lokacin da ake amfani da bilicin:
Ana hana melanin fitowa.
Fatar mutum tana rasa kariya daga rana.
Sinadarai suna shiga jini, suna karya garkuwar fata.
Fata na kara laushi da haske a waje, amma tana raunana a ciki.
Binciken da American Academy of Dermatology ta gudanar a 2023 ya tabbatar da cewa yawan amfani da hydroƙuinone da steroids na iya janyo canjin kwayoyin halitta da cutar ochronosis.
4. Shin bilicin na da amfani?
A lokacin farko da mutum ya fara amfani da kayan bilicin, zai iya ganin fata ta yi haske da laushi har ma zai iya samun gushewar ƙuraje da gishirin fuska ko maiƙo. Amma masana sun tabbatar da cewa:
Wannan canji na wucin gadi ne.
Sinadarai na taruwa a jiki har su kai ga lalata fata da wasu sassan jiki.
Ba ya ƙara lafiyar fata, illa dai sauya launin ta da karya kariyarta.
Dr. Yusuf Garba, malami a fannin sinadarai, Jami’ar Ahmadu Bello Zaria ya ce, “Bilicin ba ya ƙara lafiyar fata. Yana hana jiki kare kansa, kuma yana iya haifar da haɗurran da ba a lura da su sai daga baya.”
5. Illolin bilicin tare da hujjoji daga masana:
Ga wasu daga cikin illolin da masana suka tabbatar da su:
Canjin launin fata daga fari zuwa baƙi bayan dogon amfani da tabbatuwar tabo.
Rashin daidaiton fata, sassan fata na zama da duhu ko haske fiye da juna, ma’ana kala biyu.
Kumburi, ƙaiƙayi da tsiro, kamar eczema da fungal infections.
Kansar fata, musamman daga haɗuwar mercury da rana.
Lalacewar ƙoda, hanta da huhu, sakamakon sinadaran da suka taru a jiki.
A cewar WHO (2021): “Fiye da kashi 40% na mata a yankin Sub-Saharan Africa suna amfani da kayan bilicin da ke ɗauke da mercury, wanda ke haddasa matsaloli na ciki da waje.”
6. Shawara ga masu sha’awar yin bilicin:
Maimakon bin hanyoyin da za su iya cutar da fata da lafiya, masana sun bada shawara kamar haka:
Kula da fata ta hanyar tsafta da abinci mai gina jiki.
Gujewa kayan da ba su da rajistar NAFDAC ko sahalewar likita.
Karɓar launin fata da godiya da yadda Allah ya halicce ka.
Fahimtar cewa kyau ba launin fata ba ne, asalin kyau na nufin lafiyar fata.
Dr. Aisha Bello, dermatologist ta faɗa cewa, “Fata mai lafiya na da daraja fiye da fata mai haske amma cike da tabo da rauni.”
