
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Tinubu ya ce zai yi maraba da Ministan Abuja, Nyesom Wike zuwa cikin jam’iyyar APC a duk lokacin da ya so sauya sheƙa zuwa gare ta.
A lokacin da ya ke jagorantar ƙaddamar da hanyar Arterila Road N16 da wasu muhimman ayyuka a Gundumar Kampe dake birnin tarayya, Tinubu ya yaba wa Wike bisa gudumawarsa ga shugabanci, wanda hakan ya samo asali ne daga jajircewarsa a muƙaman da ya riƙe a baya.
Shugaba Tinubu ya ce, duk ranar da wike ya sauya ra’ayinsa zuwa komawa APC, hakan zai sa su fara waƙar “as e dey pain them, e dey sweet us”. Lamarin da ya sa jama’ar da ke wajen suka fashe da dariya har da Wike da kansa.
Wike a matsayinsa na ɗan PDP ya zama ƙarfen ƙafa a harkar siyasa musamman ga jam’iyyarsa tun a shekarar 2023 da ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu a zaɓen Shugaban Ƙasa.
Duk da cewa bai fice daga jam’iyyar ba, Wike ya karɓi muƙamin minista a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, a watan Agustan 2023.
Matakin da Wike ya ɗauka na yi wa APC aiki alhalin yana ɗan jam’iyyar adawa ya yi sanadin zurfafa rikicin cikin gida a tsakanin ƴaƴan PDP.
Haka kuma, Wike ya ci alwashin jagorantar yi wa Shugaba Tinubu yawon neman zaɓe a karo na biyu a jiharsa ta Ribas a yayin da shirye-shiryen zaɓen 2027 ke gudana.
