
Daga BELLO A. BABAJI
Wata tanka da ke maƙare da man fetur ta faɗi tare da tarwatsewa akan babban titin Legas zuwa Ibadan.
Hukumar Kiyaye Haɗurra (FRSC) reshen Jihar Ogun ta tabbatar aukuwar al’amarin ga jaridar NewsPoint Nigeria, ranar Laraba.
FRSC ta ce, lamarin ya auku ne a daidai wajen juyawa na NASFATU dake babbar hanyar.
Jami’ar Ilimantarwa ta Hukumar a jihar, Florence Okpe ta ce tuni jami’an bada agajin gaggawa da na Hukumar kashe gobara suka je wajen da abin ya faru, amma ba su tabbatar da wani asara ba.
Fashewar tankar ta shafi ababen hawa da ke kusa da ita a lokacin da abin ya faru.
Haka kuma, Faruwar al’amarin ya haifar da cinkosn zirga-zirgar al’umma a ababen hawa da makamantansu.
Al’amarin ya faru ne ƙasa da kwana ɗaya da wata tanka ta tarwatse a makarantar Muslim Grammar dake Odinjo a ƙarshen garin Ibadan a babbar hanyar.
