Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
An rantsar da sabon shugaban ƙaramar hukumar Bakori Abubakar Garba Musa bayan kwanaki biyu da rasuwar shugaban ƙaramar hukumar marigayi Aminu Ɗan Hamidu.
Ya amshi rantsuwar ne a ɗakin taro na gidan gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin sakataren gwamnatin jihar Barista Abdullahi Garba Faskari wanda ya wakilci gwamna Dikko Raɗɗa.
Da yake wa manema labarai bayani jim kaɗan da rantsar da shi, sabon shugaban ƙaramar hukumar yayi alƙawarin cigaba da ayyukan da marigayi Ɗan Hamidu ya bari na cigaban yankin.
Haka kuma yayi alƙawarin tafiya da mutanen marigayin ba tare da nuna wani banbanci.
“Zan cigaba da dukkan ayyukan da marigayi ya fara da wanda bai fara ba domin cigaban al’ummar ƙaramar hukumar Bakori da Jihar Katsina baki ɗaya”,inji shugaba Abubakar Musa.
Ya bayyana cewa ƙaramar hukumar Bakori tayi babban rashi na shugaba adali mai gaskiya da riƙon amana gashi da son jama’a.
Sabon shugaban ƙaramar hukumar wanda yana magana yana zubar da hawaye ya ce”Watanni uku da hawan kujerar shugabancin ƙaramar hukumar marigayi Ɗan Hamidu ya taɓa harkokin ilmi, kiwon lafiya da koyawa matasa sana’o’i,” inji Abubakar Musa.
Kafin rantsuwar sa Abubakar Garba Musa shine mataimakin shugaban ƙaramar hukumar na Bakori.
Kwamishinoni, shugabannin ƙananan hukumomi da sauran manyan jami’an gwamnati suka halarci bikin rantsuwan.
