
Daga BELLO A. BABAJI
Kotun Ɗaukaka ƙarar a Abuja, ta kori bututuwa guda biyu da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya shigar da cin sa tarar Naira 100,000.
A wani hukunci na tawagar alƙalai guda uku ƙarƙashin jagorancin Hamman Barka, an yi watsi da buƙatar Akpabio na rana 21 ga watan Mayu, 2025 biyo bayan neman janye ƙarar da aka yi.
Takardun ƙarar masu ɗauke ranakun 3 ga watan Maris, 2025, da 25 ga Maris, 2025, masu lambobin CV/395/M1/2025 da CV/395/M2/2025, suna ɗauke ne da sunan Akpabio a matsayin wanda ya shigar da ƙara.
Waɗanda aka shigar da su ƙara sune: Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, akawon majalisa, Majalisar Dattawa da shugaban kwamitin ladabtarwa na majalisar, Sanata Neda Imasuem.
A yayin hukunci, kotun ta yanke karɓar ƙorafin da ke neman a janye ƙarar akan waɗanda Akpabio ya zayyano, inda ta yi watsa da ƙararrakin.
Sannan, ta umarci shugaban Majalisar Dattawan ya biya Natasha tarar Naira 100,000.
