
Daga BELLO A. BABAJI
A safiyar ranar Alhamis da misalin ƙarfe 7 na safe ne Shugaba Bola Ahmed zai yi wa ƴan Nijeriya jawabi, wanda hakan wani ɓangare ne na bikin Ranar Demukraɗiyya na 2025.
Haka kuma zai halarci taron haɗaka na Majalisar Dattawa da ta Wakilai a zauren majalisa dake Abuja a ranar.
Kwamitin ministoci akan Ranar Demukraɗiyya ya bayyana hakan a wata takarda, ranar Laraba.
Abdulhakeem Adeoye wanda ya miƙa takardar a madadin jami’in hulɗa da jama’a na kwamitin, ya ce ba za yi fareti ba, saidai za a gabatar da lakca mai taken ‘Consolidating on the Gains of Nigeria’s Democracy: Necessity of Enduring Reforms’ a ɗakin taro na Fadar Shugaban Ƙasa da misalin ƙarfe 4 na yamma.
Ranar Demukraɗiyya ta wannan shekarar ta yi daidai da cikar Nijeriya shekaru 26 ana mulkin farar hula ba gare da tsaiko ba biyo bayan kawo ƙarshen mulkin soja a shekarar 1999.
