June 12: Za a yi zanga-zangar tsadar rayuwa da rashin tsaro a jihohi 20, inji masu shiryawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Yayin da ake gudanar da shirye-shiryen bikin Ranar Demukraɗiyya a Nijeriya, ƙungiyar #TakeItBackMovement ta shirya yin zanga-zanga a ranar Alhamis.

A jiya ne waɗanda suka shirya ta suka fitar da jaddawalin wuraren da za a haɗu kuma a gudanar da zanga-zangar.

An ayyana ranar ‘June 12’ a matsayin Ranar Demukraɗiyya a shekarar 2018 a ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, domin karrama marigayi Moshood Abiola, wanda shi ne ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa na 12 ga wata Yuni, 1993.

Masu shiryawar sun ce, za a yi zanga-zangar ne domin nuna ƙin amincewa da halin matsin rayuwa da rashin tsaro da al’ummar ƙasa suke fuskanta a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed.

Kodinetan tafiyar na ƙasa, Juwon Sanyaolu ya bayyana cewa za a gudanar ne a jihohi guda 20 na Nijeriya, inda a birnin tarayya Abuja za a haɗu a Filin taro na Eagle Square daga ƙarfe 8 na safe, a yayin da a Legas kuma za a taru a wurare huɗu da suka haɗa da Badagry, Maryland, Agbara da Toll Gate daga ƙarfe 7 na safe.

Sauran wuraren sune: Cathedral Junction a Akure, Jihar Ondo da misalin ƙarfe 8:00, Museum Ground a Benin City, Jihar Edo da ƙarfe 9:00 na safe da kuma Gidan Matasa a Jihar Neja da ƙarfe 8 na safe.

A Damaturun jihar Yobe ya ce, za taru a shataletalen Maiduguri Bypass da ƙarfe 7:30, yayin da a Ibadan, Jihar Oyo za a haɗu a Shataletalen Mokola daga 8 na safe.

A Jihar Bauchi kuwa, za a haɗu a daura da Bauchi School of ACR a Yelewam Makaranta da ƙarfe 8:00, sannan a Osogbo na Osun kuma a Olaiya Junction.

Sauran wuraren sun haɗa da Shataletalen Amukpe a Sapele da Summit Junction da kuma Koka Junction in Asaba a Jihar Delta. Sauran wurare a jihar sune “Otovwodo Junction in Ughelli, PTI Junction, Effurun and DSC Roundabouts in Warri and Police Station Junction in Abraka”, kamar yadda NewsPoint ta ruwaito.

Akwai hanyar Juppu Jam a Yola, Jihar Adamawa da kuma Gadar Kasuwar Gamboru a Borno.

By Babaji