
Daga BELLO A. BABAJI
Babban Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Ƙasa (TCN) ya sanar da kamfanonin raba lantarki (DisCos) na jihohi shida dake Arewa maso Gabas cewa za a samu ɗaukewar wuta a shiyyar a yayin da kuma za a samu ƙarancin wuta a wasu wurare na tsawon kwanaki huɗu.
A wata takarda daga manajan gudanarwa na Shiyyar Bauchi, Injiniya J.O Joseph, rage wutar ya faru ne a sakamakon tsaiko da aka samu a sababbin layukan lantarki masu ƙarfin 300kV a Bauchi.
Sanarwar ta ce hakan zai faru ne daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Yuni, wanda kuma zai shafi layin Jos-Bauchi-Gombe mai ƙarfin 132kV.
A lokacin da ya ke tabbatar da al’amarin, DisCo na Yola, ya ce ɗaukewar wutar zai shafi wasu yankunan jihohin Adamawa, Borno, Taraba da Yobe daga karfe 10 na safiyar Talata zuwa 5 na yammacin Asabar, wato 14 ga watan Yuni.
Ya ce, a yanzu layukan Ƙananan Hukumomin Damaturu, Molai, Yola da Jalingo za su kasance babu wuta.
Hakan na faru ne a sakamakon rashin wadataccen raba wuta da aka samu daga TCN da kuma aikin sake gina tashar lantarki ta Bauchi, kamar yadda Disco na Jos ya bayyana.
