Daga USMAN KAROFI
A wani fafatawa na sada zumunta da aka buga a daren Talata a filin wasa na City Ground, ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Senegal ta lallasa Ingila da ci 3-1, abin da ya sa ta kafa tarihi a matsayin ƙungiya ta farko daga nahiyar Afirka da ta doke Ingila. Harry Kane ne ya fara zura ƙwallo a ragar Senegal bayan ɗan wasan gaban Ingila, Anthony Gordon, ya gwada bugun da mai tsaron ragar ya mayar, amma Ismaila Sarr ya farke ƙwallon kafin ƙarshen rabin lokaci.
A zagaye na biyu, Habib Diarra ya ƙara ci gaba da jefa ƙwallon da ta tura Senegal gaba, yayin da Jude Bellingham ya zura ƙwallo da aka soke daga bisani bayan duba VAR da ya nuna cewa Levi Colwill ya taɓa ƙwallon da hannu. A ƙarshe, a lokacin ƙarin lokaci, Cheikh Sabaly ya zura kwallo ta uku wacce ta tabbatar da nasarar Senegal a ranar da za a daɗe ana tunawa da ita.
Wannan sakamako ya zo ne watanni uku kafin sabon zagaye na wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya, inda za a fara da karɓar bakuncin ƙasar Andorra a Villa Park ranar 6 ga Satumba, sannan su tafi wasan waje da ƙasar Serbia bayan kwana uku.
