Bill Gates, ‘Yan Ogoni da wasu sun shiga sahun mutane 959 da Tinubu zai ba wa lambar ƙasa

Spread the love

Dafa BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya amince da karrama mutane 959 da lambar girmamawa ta ƙasa.

An gudanar da haka ne a zaman Majalisar Ƙasa da ya wakana a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ranar Alhamis.

Babbar Sakatariyar Ofishin Harkokin Ministoci, Dakta Emanso Umobong ta ce an zaɓi mutane 824 don karramawar 2024/2025 da kuma wasu 135 na musamman, wanda hakan ya kai adadin zuwa 959.

Umobong ta ce, waɗanda aka karrama sun haɗa da fitattun ƴan Nijeriya da wasu daga ƙasashen waje da suke ba da gudummawa a fannoni daban-daban.

Daga cikin su akwai hamshaƙin attajiri a matakin duniya wato Bill Gates da tawagar ƴan ƙwallon kafa ta mata Super Falcons da na kwando D’Tigress da kuma Farfesa Mahmood Yakubu, wato tsohon shugaban hukumar zaɓe (INEC) da ya saukadaga muƙamin a ƴan kwanakin nan.

By Babaji