
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A jiya Alhamis ne Shugaba Bola Tinubu ya yi afuwa ga Farouk Lawan, wanda tsohon ɗan Majalisar Wakilai ne da Kotun Ƙoli ta hukunta a baya akan laifin karɓar cin hanci.
Baya ga Lawan, akwai wasu mutane guda 174 da suka samu yafiyar shugaban ƙasar ciki har da magabatan Nijeriya da suka haɗa da Herbert Macaulay da tsohon Ministan Abuja na zamanin mulkin Janar Babangida, Manjo Janar Mamman Vatsa (mai ritaya).
A shekarar 2012 aka zargi tsohon ɗan majalisar, wanda ya wakilci mazaɓar Ɓagwai/Shanono ta Jihar Kano da neman attajiri Femi Otedola ya ba shi cin hancin Dala miliyan 3, lamarin da ya saɓa wa dokar haramcin hakan.
An yi zargin cewa, ya nemi haka ne da nufin cire Kamfanin Otedola na ‘Zenon Petroleum and Gas Limited’ daga sahuh kamfanonin da ake tuhumar su da badaƙalar tallafin mai.
Cecekuce akan lamarin ya yi ƙamari ne a lokacin da aka ga wani faifan bidiyo da ke nuna yadda Lawan ke ciro dami-dami na kuɗaɗe daga riga da hularsa.
Daga bisani Hukumar kula da lamuran hana rashawa da wasu manyan laifuka (ICPC) ta gurfanar da shi akan laifuka bakwai masu alaƙa da cin hanci, inda wata Babbar Kotun Tarayya da ke Apo a Abuja ta yanke masa hukuncin shekara bakwai a gidan yari.
A watan Fabarairun 2022 ne Kotun Ɗaukaka Ƙara ta sake yin hukunci akan lamarin inda ta rage shekarun da aka yanke masa zuwa biyar, lamarin da Kotun Ƙoli ta tabbatar a watan Janairun 2024.
A watan Oktoba, 2024 tsohon ɗan majalisar ya kammala shekaru biyar ɗin da aka ɗiba masa na zaman kurkukun.
Da yake tsokaci akan yafiya da Shugaban ƙasar ya masa a wata takarda, Lawan ya miƙa godiyarsa a gare shi, inda ya kuma ce hakan wani yanayi na sabunta masa fata a al’amuran rayuwarsa na nan gaba.

