A fifita adalci kan ƙa’idoji yayin hukunci – Osinbajo ga Kotun Ƙoli

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya caccaki Kotun Ƙoli da wasu fagagen shari’a kan yadda suke fifita ƙa’idojin shari’a akan yin adalci a yayin yanke hukunci.

Ya ce, yin hakan abu ne da ke sanyaya wa al’umma gwiwa wajen fatan samun adalci a kotuna da rage martabar harkar shari’a a Nijeriya.

Farfesa Osinbajo, wanda babban lauya ne (SAN), ya bayyana haka ne a jiya Alhamis a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, yayin jawabi a taron lakcar shekara-shekara ta Farfesa Yusuf Ali da aka gudanar ƙarƙashin jagorancin Jami’ar Kwara (KWASU) a Malate.

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasar ya bayyana cewa babbar manufar samar da kowane tsari na shari’a itace a yi wa al’umma hidima ba fifita dokoki masu tsauri a hanyoyinsu ba.

Osinbajo ya ƙara da cewa, da dama daga cikin hukunce-hukuncen shari’a ciki har da na Kotun Ƙoli sun ta’allaƙa ne da tsari ba abinda ya dace ba na adalci, lamarin da a cewarsa ya ci karo da yadda ake yi a mataki na duniya.

Ya kuma bada misali da kotunan Turai, waɗanda al’adar shari’arsu Nijeriya ta gada, yana mai cewa ya zama lallai a riƙa la’akari da adalci yayin hukunci akan shari’o’i don tabbatar da gaskiya acikin haka.

By Babaji