Borno: Zulum ya umarci a gaggauta bincike akan cin zarafin mata bisa sanya hijabi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamna Umara Babagana Zulum na Jihar Borno ya umarci da gaggauta fara bincike akan zargin cin zarafin wasu matan Musulmi sakamakon sanya hijabi a yayin da suka je asibitoci a Maiduguri, babban birnin jihar.

Hakan na zuwa ne jim-kaɗan da ƙungiyar kare ƴancin al’ummar Musulmi (MURIC) ta fitar da wata sanarwa, inda ta yi ikirarin cewa da dama daga mata musulmai suna fuskantar cin zarafi da nuna wariya saboda hijabin da suke rufe jikkunansu da su yayin zuwa asibiti.

Da yake tsokaci akan rahoton, Zulumi ya bayyana kaɗuwarsa inda ya ce gwamnatinsa ba ta taɓa samun wani ƙorafi a hukumance ba akan haka, saboda haka ba za su lamunta ba.

Ya bayyana cewa, gwamnatin nasa ta ɗauki al’amarin da girman gaske wajen ganin an yi adalci akan abinda ya shafi lamarin addini.

A wata takarda daga Kakakinsa, Malam Dauda Iliya, Farfesa Zulum ya ce gwamnatin ta duƙufa wajen bada kariya ga ƴanci da mutuncin al’ummar jihar musamman mata ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.

Akan haka ne gwamnan ya umarci Kwamishinan Lafiya da Hidimar Al’umma, Farfesa Baba Mallam Gana da ya gaggauta ƙaddamar da bincike akan lamarin tare da miƙo rahotonsa nan ba da jimawa ba.

Gwamnan ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa ta ƙin lamuntar dukkan wani nau’i na nuna wariya musamman akan mata da ke ƙoƙarin bin karantawar addininsu.

By Babaji