
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A jiya Alhamis Majalisar Wakilai ta umarci kwamitocinta da su fara gudanar da bincike akan dalilan da suka sa har yanzu matatun gwamnati na Fatakwal, Warri da Kaduna basa aiki duk da cewa an yi amfani da kusan Dala biliyan 18 wajen gyaransu a tsawon shekaru ashirin.
Ɗan majalisa Oluwaseun Whingsn daga Legas ya tada batun a yayin zaman majalisar ƙarƙashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu.
Gwamnatin Tarayya tana da matatu guda huɗu, wato biyu a Fatakwal yayin da Warri da Kaduna ke da ɗai-ɗai, waɗanda dukkanin su ke karkashin kulawar Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL).
Matatun suna fama da matsalolin rashin hukumomin gudanarwa masu inganci da lalata kayayyakinsu, lamarin da ya sa Nijeriya ke dogaro da man da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje bayan tace shi..
A ƴan kwanakin nan ne sanannen Attajiri Alhaji Aliko Ɗangote ya ce damanmakin gyara matatun domin komawa aiki yadda ya dace ba su da yawa.
Ɗan majalisar, wanda ke wakiltar mazaɓar Badagry, ya bayyana kaɗuwarsa kan yadda aka kashe maƙudan kuɗaɗen wajen gyara su, amma kuma har yanzu babu wani sakamako mai nagarta da aka samu a sanadin haka.
