Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Farashin kasuwar Bitcoin ya faɗi zuwa dala 90,500 a farkon sa’o’in ciniki a ranar Litinin yayin da ake ci gaba da fuskantar matsin lamba kan rashin tabbas ɗinsa kan tattalin arzikin duniya.
Kasuwancin sayar da Bitcoin ya yi zafi sosai saboda raunin masu saka hannun jari na crypto. An samu babban faɗuwar kadari na dijital ya, wanda ya rage ƙimar komai.
Bitcoin (BTC-USD) ya yi asarar kusan kashi 4 a cikin sa’o’i 24 na ƙarshe a cikin kasuwar crypto, inda ya faɗo zuwa dala 90,500.
Mafi girman kadarar dijital ta duniya ta ƙimar kasuwa ta yi asarar kusan kashi 9 na darajar kasuwarta a kwanaki bakwai da suka gabata.
