CBN ya ci tarar bankuna tara saboda rashin saka kuɗi a ATM

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ci tarar wasu bankunan kasuwanci na Nijeriya saboda samun kuɗi a na’urorin cire kuɗi na ATM ɗinsu a lokacin bukuwan ƙarshen shekara.

Babban bankin ya tarar naira miliyan 150 ne kan kowane banki da ya samu da laifin, kuma bankunan sun haɗa da Fidelity da First Bank Plc da Keystone da Union da Globus da Proɓidus da Zenith Bank da UBA da Sterling tarar naira miliyan 150.

A wata sanarwa da aka miƙa wa bankunan, an ce za a zare kuɗaɗen ne kai tsare daga asusun ajiyan bankunan da ke babban bankin.

“CBN ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen cin tarar duk wani bankin da ya karya dokar tabbatar da yalwatar kuɗaɗe,” kamar yadda mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na bankin, Hakama Sidi Ali ya tabbatar.

Ya kuma ƙara da cewa, za su cigaba da bibiyar masu ɓoye tsabar kuɗaɗe a bankuna da masu POS.

Muƙaddashin daraktan yaɗa labarai na babban bankin na CBN, Madam Hakama Sidi Ali, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce, “Tabbatar da kuɗaɗen da ba su dace ba, yana da muhimmanci wajen tabbatar da amincin jama’a da kuma daidaita tattalin arzikin ƙasa.

“CBN ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ƙara sanyawa duk wata cibiya da aka samu da karya ƙa’idojin rarraba kuɗaɗe.”

Binciken da kuma sa ido na CBN zai ci gaba da binciki yadda ake tara kuɗaɗe da rabon kuɗaɗe, a rassan banki da kuma masu gudanar da ayyukan tallace-tallace (POS). Babban bankin yana aiki tare da hukumomin tsaro don daƙile tallace-tallacen tsabar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba da kuma cin zarafi na aiki, gami da tilasta ma’aikatan POS.

Babban bankin na CBN, Gwamna Olayemi Cardoso, a jawabinsa a wajen bikin cin abincin ma’aikata na shekara-shekara da aka gudanar a cibiyar Chartered Institute of Bankers of Nigeria (CIBN) a watan Nuwamba 2024, ya gargadi bankunan da su bi ƙa’idojin raba kuɗaɗe ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani.

Ya jaddada ƙudirin bankin na CBN na ci gaba da tsare tsare-tsaren kuɗi domin biyan buƙatun ‘yan Nijeriya.

Cardoso ya ce, “Mayar da hankalinmu ya kasance kan inganta amana, tabbatar da kwanciyar hankali, da kuma ba da tabbacin zagayawar tsabar kuɗi a cikin tsarin hada-hadar kudi,” inji Cardoso.

Babban bankin na CBN ya buƙaci ɗaukacin cibiyoyin hada-hadar kuɗi da su bi ƙa’idojin sa, inda ya yi gargaɗin cewa ci gaba da cin zarafi zai jawo ƙaƙaba mata takunkumi cikin gaggawa.

By ukarofi