Wutar lantarkin Nijeriya ya ragu zuwa megawat 4,500 duk da lamunin Dala biliyan 3.23

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wutar lantarkin Nijeriya na ci gaba da yin raguwa a kusan megawatt 4,500 duk da cewa ƙasar ta samu lamuni da ya kai dala biliyan 3.23 a cikin kimanin shekaru huɗu daga cibiyoyin hada-hadar kuɗi na duniya.

Cibiyoyin duniya irin su Bankin Duniya, Bankin Raya Afirka, da Hukumar Hadin Kan ƙasa da ƙasa ta Japan, sun tallafa wa fannin wutar lantarki da lamuni na biliyoyin daloli, amma har yanzu sassa da dama na Nijeriya na fama da matsalar rashin wutar lantarki.

An amince da waɗannan kuɗaɗe ne don gudanar da ayyuka daban-daban don magance ƙalubalen wutar lantarki a ƙasar da inganta samar da ingantaccen wutar lantarki.

Amma duk da haka, samar da wutar lantarki a ƙasar ya ci gaba da yin raguwa a kusan megawatt 4,500 ga al’ummar sama da mutane miliyan 200.

Rahoton wutar lantarki na yau da kullum da aka samu ya nuna cewa ƙarfin da aka samu ya kai megawatt 4,743 ya zuwa ƙarfe 6 na safiyar Alhamis.

Duk da haka, matsakaicin wutar lantarki a cikin shekaru uku da suka gabata ya kasance a kan 4,500MW duk da kokarin da gwamnati ta yi.

Tun daga shekarar 2020, bankin duniya ya amince da lamuni da yawa ga bangaren wutar lantarki na Nijeriya, yana mai da hankali kan hanyoyin samar da makamashi mai ɗorewa, inganta tsarin rarrabawa, da sake fasalin sassan gaba ɗaya.

A watan Satumbar 2024 ne aka rattaba hannu kan shirin samar da wutar lantarki mai ɗorewa da ban ruwa ga Nijeriya, tare da babban adadin dala miliyan 500, don inganta amincin makamashi.

By ukarofi