Boko Haram sun harba rokoki a Maiduguri gabanin ziyarar Buhari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Mayaƙan Boko Haram sun kai hari Maiduguri babban birnin jihar Borno gabanin ziyarar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

An ce, maharan sun kai hari kan wasu al’ummomi uku a babban yankin filin jirgin sama na Ngomari da ke Maiduguri.

Ga dukkan alamu maharan sun nufi filin jirgin ne yayin da suka kai hari da misalin ƙarfe 10:45 na safe, mintuna kaɗan kafin isowar Buhari.

Wasu mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa, maharan sun afka wa al’ummomin da makaman roka, inda suka kashe mutane da ba a tabbatar da adadinsu ba, tare da lalata unguwanni da kadarori.

Wani mazaunin garin ya ce, ɗaya daga cikin rokokin ya faɗa kusa da wani ofishi, biyu kuma sun faɗa a unguwar Ngomari Ayashe, inda suka kashe yara huɗu, ɗaya a Moranti.

“Zan iya tabbatar da cewa wani yaro mai shekaru 16, Walida, ya jikkata a harin. Wata yarinya kuma ta mutu nan take, tana cikin girki ne rokar ya lalata mata kai,” inji mazaunin garin.

Aƙalla mutane 25 aka ruwaito sun samu raunuka a harin, wanda har yanzu hukumomi ba su ce uffan ba.