Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wasu ‘yan ta’addan Boko Haram ɗauke da makamai sun kai farmaki garin Kirawa da ke kan iyaka da jamhuriyar Kamaru a ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno, inda suka kashe wasu fararen hula biyu, yayin da kuma suka yi awon gaba da wani mazaunin garin.
‘Yan ta’addan sun kuma ƙona gidaje da dama ciki har da fadar Hakimin Kirawa, Alhaji Abdulrahaman Abubakar.
Da yawa daga cikin mazauna yankin da suka tsere zuwa cikin al’ummomin ƙasar Kamaru domin tsira da rayukansu, sun yaba da ƙoƙarin da wasu ‘yan ƙungiyar Ciɓilian Joint Task Force (CJTF) da mafarauta suka yi, inda suka daƙile harin, wanda kuma ya kai ga kashe ɗaya daga cikin maharan.
Kwanaki uku da suka gabata ne wasu ‘yan ta’adda suka yi kwanton ɓauna a kan hanyar Kirawa zuwa Pulka inda suka kashe jami’in CJTF ɗaya bayan sun ƙona motoci shida.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya ce: “Sabobin hare-haren Boko Haram a garin Kirawa da sauran al’ummomi ya zama abin damuwa da takaici, domin da yawa daga cikin ‘yan gudun hijirar da suka koma gidajen kakanninsu da Gwamna Babagana Zulum ya samu kuma ya tallafa musu.”
Yayin da yake yaba wa ƙoƙarin sojojin Nijeriya a yaƙin da suke yi da Boko Haram/ISWAP a yankin arewa maso gabas, Sanata Ndume, tsohon shugaban kwamitin majalisar dattawa kan sojoji, ya yi kira ga hukumomin sojin da su “aike da ƙarin sojoji ko kuma runduna a yankunan Kirawa, Ngoshe, Agapalwa, Chikide da sauran al’ummomi masu rauni”.
Ya kuma ƙara jaddada kiransa ga gwamnatin tarayya da sojojin Nijeriya da su tura jiragen sama marasa matuƙa, da kai farmakin jiragen sama masu saukar ungulu, tare da yin amfani da fasaha, kayan aiki, makamai da alburusai, ƙarfafa gwiwa, wanda shi ne kaɗai hanyar da za ta kawo ƙarshen ta’addancin ‘yan Boko Haram shekaru da dama da suka gabata a Borno, Arewa maso Gabas da sauran sassan ƙasar nan.
