Bom ya halaka mutum 20 a mashayar Taraba

Daga BASHIR ISAH

A ƙalla mutum ashirin ne aka ruwaito sun rasa rayukansu sakamakon tashin bom a wata mashayar burkutu da ke ƙauyen Iwari cikin ƙaramar hukumar Ardo-Kola a jihar Taraba.

Wani ganau ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa, wasu da dama sun jikkata sakamakon harin.

“Sama da mutum ashirin ne aka kashe a wannan yammaci a wata mashayar burkutu bayan da wani matashi ya tashi wani abu mai fashewa a mashayar da ke yankin Iware cikin Ƙaramar Hukunar Ardokola a jihar.

“Haka nan, fashewar ta jikkata wasu da dama wanda a yanzu haka ake yi musu magani a cibiyoyin kula da lafiya a Iware,” in ji majiyarmu.

Majiyar ta ƙara da cewa an kwashi gawarwakin wadanda suka mutu a harin zuwa Babbar Cibiyar Karɓar Magani ta Tarayya (FMC) da ke Jalingo.

Kazalika, majiyar ta ce fusatattun matasan Iwari sun halaka matashin da aka ce shi ne ya tashi bom ɗin har lahira.

Da aka nemi jin ta bakinsa kan batun, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Taraba ya tabbatar da faruwar haka, amma ya ce mutum uku ne suka mutu yayin da 19 suka jikkata.