Daga AISHA ASAS
A wani muhimmin mataki na cigaba a masana’antar fim ta Kudu, wato Nollywood shi ne yadda taron Best of Nollywood Awards (BON Awards) ke ƙara samun tagomashi da kuma ƙwarewa, inda a bana ma suka ɗaura aniyyar gabatar da shi cikin ƙwarewa da kuma adalci.
Rahotanni bayyana cewa, yanzu haka an bayyana sunayen yan takara a kowane ɓangare inda aka bayyana fim ɗin ‘Seven Doors’ a matsayin fim ɗin da ya shiga ɓangare har tara don fafatawa, wanda hakan ma babbar nasara ce ga fim ɗin tun a matakin farko.
Fim ɗin ‘Abanisete ya biyo baya da shiga guraben takara takwas, yayin da sauran manyan suke cikin jeri daban-daban.
An kuma sanar da cewa bikin karramawa da bayar da lambobin yabon zai gudanar ne a ranar 14 Disamba 2025 a otel ɗin Federal Palace da ke Victoria Island, Lagos. Masu shirya kyaututtukan sun ce wannan ya zama wata dama ta musamman ga masana’antar fim ta Najeriya don nuna sabbin fasaha, ƙirƙira, da hazaƙa.
Masana fim na Najeriya sun bayyana cewa sunayen na bana sun nuna yadda masana’antar ke canzawa — daga yawan samar da fim zuwa inganci, wanda ya haɗa da bincike da kuma neman haɗin gwiwa da ƙasashen waje. Amma duk da haka, ƙalubale na wurin rarrabuwar kudade, rarraba fina‑finai da sayar da su na waje ya ci gaba da kasancewa mai tsanani.
