
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Gwamnatin jihar Borno ta janye dokar hana fita a faɗi jihar wanda ta sanya sakamakon hargitsi da ake samu a yayin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya.
Hakan na zuwa ne bayan da aka samu sace-sace da ƙone-ƙone a wasu sassan ƙasar inda gwamnan jihar, Umar Babagana Zulum ya sanya dokar kulle na sa’o’i 24 don dakatar da aukuwar fitina a faɗin jihar.
Zulum ya yi jawabin ne a wata hirar kai-tsaye da ya gabatar, ya na mai cewa hakan dama ce ga al’umma su fito su cigaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda aka saba wanda su ka yi tare da haɗin-gwiwar hukumomin tsaro.
Ya kuma ce, ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda aka samu da hannu a cikin karya doka da oda da sunan zanga-zanga a faɗin jihar.
