
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya zargi cewa kashi 95 na waɗanda su ka yi zanga-zanga a ranar Alhamis a jihar ƴan ƙasa da shekaru 14 ne.
Gwamnan ya faɗi haka ne a lokacin da ya ke gabatar wani jawabi na kai-tsaye a ranar Asabar a inda ya ɗage batun dokar hana fita.
Ya ce, “abin mamaki ne ganin ɗan shekara shida ɗauke da allo wanda tabbas wani ne ya umarce shi. Mafi yawancin irin waɗannan yaran, ba ƴan Borno ba ne.”
Zulum ya ce akwai buƙatar duba lamarin dubban yaran da ke zama a Maiduguri da sunan almajiranci.
Haka nan, ya ce ɓata-gari da su ka sauya zanga-zangar zuwa tashin-tashina, sun lalata ababe da dama da kuma satar dukiyar al’umma ciki da hara da a asibitoci.
Kazalika, gwamnan ya ƙara jaddada ƙoƙarin gwamnatinsa na inganta harkoki da dama a jihar ciki har da ɓangarorin kiwon lafiya da ilimi.
