‘Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga da borkonon tsohuwa a Abuja

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Jami’an ‘Yan sanda sun tarwatsa taron masu zanga-zanga a filin MKO Abiola da ke Abuja, bayan da su ka watsa mu su hayaƙi mai sanya ƙwalla.

An samu raguwar adadin waɗanda su ka halarci zanga-zangar idan an kwatanta da ranakun Alhamis da Juma’a inda bayan da su ka taru a filin da su ka saba yi ne, sai jami’an su ka nemi tarwatsa su ta hanyar amfani da borkonon.

Haka kuma, a ranar Juma’a ma an yi mu su irin haka a lokacin da su ka taru a Shataletalen Berger da ke cikin garin Abuja.

Yayin da ake samun faruwar ire-iren haka a wurare mabanbanta, adadin masu zanga-zangar na raguwa a dai-dai lokacin da ƴan ƙasa ke cigaba da nuna rashin amincewa da halin tsadar rayuwa da ake ciki a sassa daban-daban na faɗin Nijeriya.

By Babaji