Buhari ya rantsar da Arase a matsayin Shugaban PSC

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya rantsar da tsohon Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Solomon Arase, a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kula da Harkokin ‘Yan Sanda (PSC).

Buhari ya rantsar da Arase ne gabanin zaman Majalisar Zartawa ranar Laraba a Abuja.

Rantsarwar na zuwa ne bayan tabbatar da cancantarsa da Majalisar Dattawa ta yi watanni biyu da suka shuɗe.

Buhari ya miƙa sunan Arase ga Majalisar Dattawa don neman yardarta kan naɗin daidai da sassa na 153 (1) da 154 (1) na kundin tsarin mulkin ƙasa wanda aka yi wa kwaskwarima.

Arase, mai shekaru 65 da haihuwa, ya yi ritaya daga aiki a 2016 a matsayin Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda na 18, inda ya riƙe wannan matsayi daga Afrilun 2015 zuwa Yunin 2016.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *