Buhari ya sauka a Maiduguri duk da hare-hare

*Boko Haram ta harba rokoki da boma-bomai kafin saukar Shugaban Ƙasar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, a jiya Alhamis, ya kai ziyarar aiki ta yini guda da kuma ƙaddamar da wasu ayyuka da Gwamnatin Jihar Borno ta aiwatar a Maiduguri, Babban Birnin Jihar, mintuna kaɗan bayan ’yan Boko Haram sun harba roka cikin filin jirgin sama na Maiduguri ɗin.

Manyan ma’aikatan gwamnati sun yi wa Buhari rakiya zuwa Bornon, inda jirginsa ya dira da misalin ƙarfe 11.45 na safiyar ranar Alhamis.

An samu shakkun cewa, ko shugaba Buhari zai sauka a Maiduguri yayin da wasu boma-bomai uku suka tashi a birnin sa’o’i kaɗan kafin isowarsa.

Wani babban kwamandan soji ya ci gaba da gudanar da jadawalinsa na isowar shugaban kamar yadda aka tsara zai fara ne da ƙaddamar da wani gini da Mohammed Indimi ya bayar ga jami’ar Maiduguri.

Bayan haka, zai ci gaba da ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar Borno ta aiwatar da suka haɗa da titin mota mai tsawon kilomita 10, gadar sama, da babbar makarantar sakandare.

A cewar mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin soshiyal midiya, Bashir Ahmad, shugaban ƙasar zai kuma samu rahotannin farko daga sojojin Nijeriya da ke yaƙi da ‘yan ta’addan Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.

A halin da ake ciki dai fashe-fashen da wasu ke fargabar ka iya sa shugaban ya soke tafiyar tasa a Maiduguri, lamarin ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutane huɗu.

Gwamna Zulum ya tarbi Buhari:
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya ziyarci filin jirgin tare da dukkan shugabannin tsaro, da suka isa jihar domin tarbar Buhari.

Wannan ziyarar ita ce ta biyu da Buhari ke kai wa Borno cikin watanni 6 da suka gabata tun ziyarar da ya kai ƙarshe a ranar 21 ga watan Yunin 2021 inda ya ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin ta yi da NEDC.

Nan take aka ɗauki Shugaban ƙasar a mota daga filin jirgin zuwa babban makarantar Shiekh Tijanni Bolori da ke bayan Quarter Maiduguri.

Zulum ya yi kira ga al’ummar jiharsa su fito ƙwansu da ƙwarƙwata su tarbi Shugaba Buhari a ƙoƙarin da ake yi na mayar da su gidajensu da kuma ayyukan alheri da shugaban ƙasar ya yi musu a shekaru shida da suka gabata.

An gano cewa, an bada umurnin rufe wasu hanyoyi da kasuwanni da ke cikin birnin yayin ziyarar shugaban ƙasar har sai ya tafi misalin ƙarfe 2 na rana.

Boko Haram sun harba rokoki mintuna kaɗan kafin ziyarar:
Mayaƙan Boko Haram sun kai hari Maiduguri babban birnin jihar Borno gabanin ziyarar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

An ce, maharan sun kai hari kan wasu al’ummomi uku a babban yankin filin jirgin sama na Ngomari da ke Maiduguri.

Ga dukkan alamu maharan sun nufi filin jirgin ne yayin da suka kai hari da misalin ƙarfe 10:45 na safe, mintuna kaɗan kafin isowar Buhari.

Wasu mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa, maharan sun afka wa al’ummomin da makaman roka, inda suka kashe mutane da ba a tabbatar da adadinsu ba, tare da lalata unguwanni da kadarori.

Wani mazaunin garin ya ce, ɗaya daga cikin rokokin ya faɗa kusa da wani ofishi, biyu kuma sun faɗa a unguwar Ngomari Ayashe, inda suka kashe yara huɗu, ɗaya a Moranti.

“Zan iya tabbatar da cewa wani yaro mai shekaru 16, Walida, ya jikkata a harin. Wata yarinya kuma ta mutu nan take, tana cikin girki ne rokar ya lalata mata kai,” inji mazaunin garin.

Aƙalla mutane 25 aka ruwaito sun samu raunuka a harin, wanda har yanzu hukumomi ba su ce uffan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *