Buhari ya tsawaita wa’adin tsohuwar N200

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince a ci gaba da amfani da tsohuwar N200 nan da wata biyu.

Ya bayyana haka ne yayin jawabin da ya yi wa ‘yan ƙasa kai tsaye da safiyar Alhamis.

Buhari ya ce ya tsawaita wa’adin amfani da N200 ne domin rage wa ‘yan ƙasa raɗaɗin ƙarancin kuɗin da ake fuskanta a faɗin ƙasa.

A cewarsa, za a ci gaba da amfani da N200 ne daga ran 10 Fabrairu zuwa 10 ga Afrilun 2023.

Sai ƙarin wa’adin in ji Buhar, bai shafi tsoffin N500 da N100 ba.

Shugaban ya ce ƙofar CBN a buɗe take domin ci gaba da karɓar tsoffin takardun kuɗi na N500 da N1000.