Tsoffin kuɗi: Gwamnatin Kaduna ta sake shigar da ƙara kan Gwamnatin Tarayya

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Jihar Kaduna, ta hannun lauyanta Abdulhakeem Mustapha SAN, ta shigar da ƙara kan Gwamnatin Tarayya saboda rashin kiyaye umarnin kotu.

Wannan na zuwa ne kwanaki bayan da Gwamnatin Kaduna tare da takwarorinta Kogi da Zamfara suka maka Gwamnatin a Kotun Ƙoli dangane da matakin canjin kuɗin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ɗauka wanda hakan ya haifar da ƙarancin kuɗi a faɗin ƙasa.

Yayin zaman kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Justice Inyang Okoro, Mustapha musta ya ja hankalin kotun kan zargin da ya yi cewa Gwamnatin Tarayya ba ta martaba umarnin da kotun ta bayar a makon jiya ba na tsawaita wa’adin ci gaba da amfani da tsofaffin takardun Naira.

Sai dai lauyan Gwamnatin Tarayya, Kanu Agabi, ya musanta zargin, yana mai cewa an gina tuhumar ce kan jita-jita.

Majalisar alƙalan da ke sauraren shari’ar ta ce bai yiwuwa a saurari batun nan take har sai an kammala cika sharuɗɗan da suka kamata wajen shigar da ƙara.

Sai dai kuma lauya Mustapha haƙiƙance kan cewa Gwamnatin na sakaci wajen ƙin martaba umarnin na kotu.

Don haka ya dage kan lallai sai dai a tsawaita wa’adin amfani da tsofaffin kuɗin.