
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar jagororin kasuwanci da masana’antu ta Africa CEO Club (ACC) ta jagoranci babban taron tattaunawa na jagorancin mata a ranar 30 ga watan Oktoba, 2025.
An yi wa taron na ‘High-Level Women’s Leadership Dialogue’ laƙabi da ‘Africa: Her Voice, Her Power’, wato Afirka: muryarta, ƙarfinta, wanda aka gudanar a Afreximbank African Trade Center Headquarters da ke Abuja.
Taron ya samu halartar matan gwamnoni, ministoci, gwamnoni, jagororin kasuwanci da masana’antu, masana harkar difulomasiyya, masu samar da tsare-tsare da sauransu daga sassa daban-daban na Nahiyar Afirka.
Manufar taron ita ce jinjina da ɗaukaka muryoyin mata da ke ƙoƙarin inganta harkokin jagoranci, kasuwanci da shugabanci a nahiyar domin faɗaɗa hanyoyin nasararsu acikin al’umma.
Sannan, an shirya taron ne da haɗin-gwiwar Ƙungiyar kasuwanci, masana’antu, haƙar ma’adinai da noma (NACCIMA), Cibiyar Al’adu ta Turai (ECC) da sauran su.
Da take jawabi, Shugabar ACC, Dakta Fatoumatta Gaye ta bayyana taron a matsayin lokaci na karrama jagorancin mata a fannoni lamuran al’umma daban-daban, wanda matuƙar suka inganta, ƙasa za ta yi nasara a harkokinta na ci-gaba.
Ta bayyana cewa, inganta mata bai taƙaitu a damawa da su ba, saidai abu ne da ya shafi hatta nasarar tattalin arziƙin ƙasa don haka wajibi ne a ba fannin muhimmanci don amfaninsa ga al’umma.
Kazalika, ta yaba wa abokan hulɗa musamman wanda ya ɗauki nauyin maudu’in taron, wato All Prime Technology da US-Africa Trade Council, European Union, European Cultural Centre da dukkanin masu haɗaka da ACC.



