
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tawagar tsaro na hukumomin leƙen asiri a Nijeriya ta faɗaɗa bincikenta game da zargin ayyukan da ke neman kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, inda ta sanya wasu tsofaffin jagororin mayaƙa guda huɗu da wani babban jami’in Amnesty mai ritaya a sahun waɗanda ake sanya ido akansu.
A cewar sahihan majiyoyin sirri da suka gana da jaridar NewsPointNigeria, Hukumomin DSS da DIA suna sa ido akan mutanen waɗanda aka sa su ƙarƙashin mutane masu damuwa ta musamman wato ‘Persons of Specific Concern’ saboda alaƙarsu da wasu manyan sojoji da ake gudanar da bincike akansu a halin yanzu.
Makusanta tsaro sun shaida cewa uku daga cikin tsofaffin jagororin mayaƙan sun taɓa shiga sahun ƴan ‘Big Five’ domin ci-gaban ƙungiyar mayaƙa da ya kai ga shirin Amnesty na shugaban ƙasa na 2009 ƙarƙashin marigayi tsohon Shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’Adua.
Biyu daga cikinsu ƴan jihar Ribas ne, sai ɗaya daga Bayelsa da kuma na ƙarshen daga Ondo.
Sai kuma wani soja mai ritaya da ya taɓa jagorantar ofishin kare ƴancin al’umma na shugaban ƙasa, wato ‘Presidential Amnesty’, wanda shi ma ana sanya ido akansa.
Ɗaya daga cikin jami’an da aka kama da ke hannun DSS, ya jima yana alaƙa da ɗaya daga cikin manyan mayaƙan na Neja-Delta, wadda tana da dangantaka da shirye-shiryen tsaro na tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Bayelsa, Timipre Sylva a 2015.
Majiyoyi sun bayyana cewa, ana zargin mutanen ne bisa halartar wata ganawa da tsararren jami’in soja: ɗaya a Kaduna, ɗaya kuma a Minna da ke Jihar Neja.
A ƴan kwanakin nan ne kafafen yaɗa labarai suka fitar rahotannin zargin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, lamarin da hedikwatar tsaro da musanta.
