
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumomin wasanni a ƙasar Sifaniya sun zargi ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona da hannu a rashawa da badaƙalar kuɗaɗe.
Ana zargin Barcelona ne da bada wasu kuɗaɗe ga José María Enriquez Negreira, wanda shu ne shugaban kwamitin alƙalai na gudanarwa, CTA.
Rahotanni sun bayyana cewa daga tsakanin shekarar 2001 zuwa 2018, ƙungiyar ta biya wasu kamfanonin Negreira da makusantansa jimillar Yuro 7.2.
Ance kuɗaɗen na ‘refereeing advisory services’, wato gudunmawar horo da ci-gaba harkar alkalancin wasanni.
Saidai masu bincike sun yi zargin cewa ƙungiyar ta bada kuɗaɗen ne domin su riƙa rinjayar jami’an wasa su ke fifita lamuranta akan na ƙungiyoyin da take karawa da su a wasanni.
A yayin shari’ar akan lamarin a wata kotu da ke Birnin Barcelona, Alƙalin ya tabbatar da tuhume-tuhumen, inda ya kuma umarci ƙungiyar da fitar takardun ainihi na kuɗaɗe tare da hujjojin da ke tabbatar da sahihancinsu.
Amma, a shekarar 2021 Barcelona ta yi ikirarin cewa ba ta da takardun yarjejeniyoyi akan batun, lamarin da ya haifar da cecekuce akan gazawarta na rashin tabbatar da gaskiya da adalci a harkokinta.
